Ana ci gaba da ambaliyar ruwa a Australia

Garin Toowomba na Australia
Image caption Ana ci gaba da ambaliyar ruwa a Australia

Ambaliyar ruwa na cigaba da mamaye Brisbane babban birnin jihar Queensland a Australia, abin da ke tilastawa dubban mutane kauracewa gidajensu.

Ambaliyar ita ce mafi muni cikin shekaru masu yawa a arewacin Australia, inda ta ke cigaba da barna.

Tun da fari dai, ambaliyar ta mamaye garin Toowomba ne da ke yammacin Brisbane inda akalla mutane goma su ka mace sannan casa'in su ka bace.

Firaministar Australia Julia Gillard ta sha alwashin taimakawa jihar.

Ana sa ran ambaliyar ruwan za ta shafi kusan mutane dubu 30 a Brisbane, inda kuma fiye da mutane dubu tara suka rasa mahallinsu