Gidaje dubu 20 na cikin hadari a kasar Ostireliya

Image caption Ambaliya a rafin birnin Brisbane

Pirimiyar jihar Queensland ta ce gidaje kimanin dubu ashirin ne ke cikin hadarin mamayewar ruwa a birnin Brisbane, hedkwatar jihar.

Ambaliyar ruwa na ci gaba da malala, ya kuma tasar ma birnin na uku mafi girma a kasar Austrailiya.

Yanzu haka dai yankin tsakiyar birnin na Brisbane ya kasance fayau, bayan da aka katse wutar lantarki, aka kuma bukaci dubban jama'a su fice, ko kuma su zauna a gida.

Ruwan dai ya mamaye birnin Ipswich wanda ke yamma da na Brisbane, cikin wani yanayi da aka bayyana da cewa na rudani.

Jama'a na daukar komatsensu

A daidai lokacin da ruwan da yayi ambaliya ke ci gaba da malala, jama'a a Birisbane na ci gaba da daukar komatsensu suna dosar wuraren da ke kan tudu domin fakewa.

Yankuna 35 ne abin ya shafa kawo yanzu - kuma wannan wata alama ce kawai ta irin abin da ka iya biyo baya.

Wannan dai ita ce ambaliya mafi muni a shekaru da dama da ta faru a kasar ta Austrailiya, ana saran gidaje dubu 20n ne ambaliyar za ta ritsa da su a lokacin da ruwan zai sake ambaliya a ranar Alhamis.

Jama'ar da suka rage a birnin na Brisbane sun shaida wa BBC cewa, ba abinda ake gani sai rufin gidaje da kuma bishiyoyi.

Victoria Johnson na zaune ne a garin Brookwater da ke kan tudu, ta kuma bayyana halni da ake ciki agarin; "Mun dan samun sauki yau, rana ta fito kuma na yi sayayya, kuma shaguna a nan sun bude kuma jama'a na kaiwa da komowa inda suke sayar da kayayyaki daban daban musamman wadanda jama'a ke matukar bukata."

Ba dai a sa ran kogin Brisbane ya kara ambaliya nan da sa'o'i 24 masu zuwa. An wayi gari da yanayi mai kyau inda rana ta haska.

Amma Pirimiya Anna Bligh, ta ce kada jama'a su shagala - a daidai lokacin da daruruwan jama'a suka bace a garin Toowomba, ta yi gargadin cewa masu aikin ceto na fuskantar babban kalubale.