Fiye da mutane 200 sun mutu a Brazil

Irin barnar da zaftarewar kala ta yi a Brazil

Akalla mutane dari biyu da talatin da bakwai ne su ka mutu a kudu maso gabashin Brazil daga jiya zuwa yau sanadiyyar ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa.

Adadin wadanda aka tabbatar da rasuwarsu ya karu ne bayanda masu agajin gaggawa suka isa garin Nova Friburgo, wanda kogin lakar da ke malala akan titunansa ya katseshi daga sauran yankunan kasar.

Masu aiko da rahotanni sun ce yanzu dai ana cikin fargabar samuwar cututtukan da gurbataccen ruwa ke yadawa kuma tuni dakarun sojin Brazil su ka fara kafa asibitoci a yankin domin kai dauki ga al'umomin.