Shari'a kan mutuwar Michael Jackson

Conrad Murray
Image caption Alkali ya haramtawa Murray gudanar da aikin likita

Wani alkali a birnin Los Angeles da ke Amurka ya umarci likitan marigayi Michael Jackson ya gurfana gaban shari'a dangane da rasuwar mawakin a shekarar 2009.

Ana tuhumar dakta Conrad Murray ne da laifin salwantar da rai ba da niyya ba, zargin da tuni ya musanta.

A zaman jin ba'asin da kotu ta shafe kwanaki shida ta na yi, ta saurari shaidu fiye da ashirin, kuma a rana ta karshe, likitoci guda biyu sun bayar da shaidar cewa dakta Murray ya sabawa tsarin kiwon lafiya.

Kotun ta ji ba'asin da ke nuna cewa, likitan ya baiwa mawakin maganin bacci mai karfin gaske, domin ya taimaka masa wajen iya yin bacci.

Alkalin Michael Paster, ya yi umarnin da aka gabatar da cikakkiyar shari'a akan batun, kuma ya dakatar da dakta Murray daga aikin likita a jihar California.

A lokacin da take barin kotun, 'yar uwar mawakin La Toya Jackson ta ce, ta yi farin ciki da sakamakon zaman sauraron ba'asin.