Obama ya yabawa mutanen da suka mutu a Arizona

Shugaba Obama da matarsa Michelle a yayin adduo'i
Image caption Obama ya yabawa wadanda suka mutu a Arizona

Shugaban Amurka Barack Obama ya jinjinawa mutanen da suka rasu sanadiyyar harbe-harben da suka faru a Arizona ranar Asabar, inda wani dan bindiga ya kashe mutane shida tare da yunkurin hallaka 'yar majalisar wakilai.

Da ya ke jawabi a taron addu'o'in tunawa da mamatan a garin Tucson, Mr. Obama ya ce kamata ya yi kisan ya yi tasiri wajen inganta muhawarar da ake yi a fagen siyasar Amurka.

Ya ce:''Idan har wannan musiba ta haifar da tunani da muhawara, kamar yadda ya kamata ace ta yin, mu yi kori mu tabbatar ta dace da wadanda muka rasa''.

Da farko dai, Mista Obama ya ziyarci asibitin da likitoci ke jiyyar 'yar majalisa Gabrielle Giffords, wacce aka harba a ka.

Ya ce ta bude idonta a karo na farko tun bayan harbin da aka yi mata.