Kotu ta dakatar da Shugaban PDP na kasa

Image caption Dr Okweslizie Nwodo

A Najeriya, wata babbar kotun jihar Enugu ta bayar da umarnin dakatar da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dokta Okwesilieze Nwodo daga mukaminsa.

Wannan hukunci dai ya biyo bayan wata kara ce da wani dan jam'iyyar PDPin da ke Enugu ya shigar. Mai shari'a Reuben Onuora na babbar kotun jihar Enugu ne, ya bayar da umarnin dakatar da shugaban jam'iyar PDPin na kasa, Dokta Okwesilieze Nwodo daga mukaminsa, ko aiwatar da wani aiki da ya jibanci wannan mukami.

Har sai an yanke hukunci kan wata kara da Mista Collins Amalu, wani dan jam'iyyar PDP a jihar Enugun ya shigar.

Umarnin ya biyo bayan bukatar hakan ne da lauyoyin mai shigar da kara suka gabatar wa kotun da fatar baki, a ran ashirin ga watan Disamban da ya gabata.

An kuma dage sauraren karar har ya zuwa ran talatin da daya ga watan nan na Janairu.

Lokacin da za a ci gaba da bin kadin karar da Mista Collins Amalu ya shigar, yana kalubalantar sahihancin kasancewar Dokta Okwesilieze Nwodo dan jam'iyyar PDP, bisa zargin cewar ba shi da katin zama cikakken dan jam'iyyar.

Hakan kuwa ana ganin tun fil'azal wani guggubi ne na rikicin shuigabanci da ya dabaibaye jam'iyyar ta PDP a jihar Enugu, kuma ya haddasa rarrabuwar ta gida biyu, tsakanin magoya bayan shugaban jam'iyyar na kasa da kuma gwamnan jihar, Mista Sullivan Chime.

Sai dai kuma wannan umarni da kotu ta bayar, ya zo ne kwana daya kacal bayan da uwar jam'iyyar PDP ta kasa ta yi ikirari cewa, an warware wannan rashin jituwa, kuma ba gara bin zago.

Masu lura da al'amuran da kan je su komo a fagen shari'a, na ganin wannan umarni na kotu zai yi tasirin ne, idan aka sami dangana shi ga wanda ya shafa. Kuma idan har ta tabbata cewa, an sulhunta bangarorin jam'iyyar PDPin a jihar Enugu, to mai yiwuwa za a iya kawar da umarnin kotun.