Zaben fitar da dan takarar shugaban kasa a PDP

Tutar jam'iyyar PDP

A Najeriya, jam`iyyar PDP mai mulkin kasar tana can ta na gudanar da babban taronta na kasa, inda wakilan jam`iyyar wato deleget-deleget za su kada kuri`ar fitar da gwanin da zai tsayawa jam'iyyar takarar shugaban kasa.

Mutane ukun da jam`iyyar ta tantance su shiga a fafata da su, su ne shugaban kasar Dakta Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da kuma Mrs. Sarah Jubril.

Bangaren tsohon mataimakin shugaban kasar dai na dari-dari da kwamitin shirya babban taron bisa zargin cewa yana cike da magoya bayan Goodluck Jonathan, amma kwamitin ya jaddada cewa zai kamanta adalci.

Kimanin wakilan jam'iyar kimanin dubu biyar ne dai za su kada kuri'a don fitar da wanda zai yi ma ta takarar shugabancin kasar a zaben da za a gudanar a watan Afrilu mai zuwa.

An sanya jam'ian tsaro cikin shirin ko-ta-kwana a wasu muhimman wurare da ke birnin Abuja, inda ake gudanar da taron.