An kori Ministan cikin gida a Tunisia

Image caption Shugaban kasar Tunisia, Ben Ali

Shugaba Ben Ali na Tunisia ya kori ministan cikin gidan kasar a cikin wasu jerin matakai a yunkurin kawo karshen jerin tarzomar da kasar ta yi fama da su a baya bayan nan.

Har wa yau Shugaban kasar ya bada sanarwar sakin wasu fursunoni da ake tsare da su a kasar.

Haka nan kuma a karon farko an baza dakaru a cikin Tunis, babban birnin kasar.

Bayan da masu zanga-zangar suka mai da hankali kan birnin Tunis a daren jiya, gwamnatin kasar ta dauki wasu matakai domin shawo kan lamarin.

Sojoji na sintiri

A karon farko an ga sojoji da motocin sulke suna sinturi a birnin.

A lokaci guda kuma, shugaban Bin Ali ya kori ministan cikin gida, sannan ya bada sanarwar sakin mutanen da aka kama a lokacin tarzomar.

Za kuma a kafa kwamiti na musamman da zai binciki zargin cin hanci da rashawa da kuma halayyar manyan jami'an gwamnati. Wannan dai wani sauyi ne na bazata idan aka kwatanta da kwanakli biyun da suka wuce, lokacin da shugaban ya bayyana tarzomar da cewa aikin 'yan ta'adda ne na kasashen waje.

Sai dai babu tabbas ko hakan zai kawo karshen rikicin.

Hankalin 'yan kasar ta Tunisia dai ya tashi sosai, kan masu zanga-zangar da 'yan sanda suka kashe duk da cewa gwamnati ta ce 'yan sandan na kare kansu ne.

Dangane da rashawa kuwa, ana ganin matsala ce ta cikin gida, don haka zai yi wuya kwamitin da aka kafa ya iya shawo kan rikicin.