Ambaliyar ruwa a kasar Brazil

Sabbin alkaluman da aka fitar a kasar Brazil na cewa, akalla mutane dari hudu da saba'in ne suka hallaka sakamakonn ambaliyar ruwa da kuma zabtarewar kasa a arewacin birnin Rio de Janeiro.

'Yan sanda dai sun ce, akwai yiwuwar a samu karuwar asarar rayuka, domin kuwa ya zuwa yanzu sun kidaya gawarwakin wadanda aka shaida ne kawai

Wakilin BBC yace fiye da ma'aikatan ceto dubu ne suka isa yankin da lamarin ya shafa, kuma masana yanayi sun ce, akwai alamun za'a samu karin ruwan sama a 'yankin da lamarin ya shafa.

A jiya Alhamis ne dai shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta ziyarci yankunan da lamarin ya shafa.