An kama sojoji 5 a jihar Filato

Soji

Rundunar tsaro ta musamman dake aiki a jihar Filato a Nijeriya, ta ce tana tuhumar wasu sojoji biyar da lafin yin sakaci wajen hana kai hari a kan wani kauye dake karamar hukumar Riyom.

Harin da aka kai zuwa kauyen yayi sanadiyar mutuwar mutane goma sha uku a cikin wannan mako.

Rundunar sojan ta ce sojojin biyar ba su yi abinda ya kamata ba wajen hana kai harin, amma ta bayyana cewa sabanin rade-radin da ake yi, ba wai tana zarginsu ne da kai harin ba.

Hare haren da aka kai kan wasu kauyuka dake kananan hukumomin Barikin Ladi da kuma Riyom din sun yi sanadiyar mutuwar jumlar mutane goma sha takwas, baya ga wasu da dama da suka rasa rayukansu a tashin hankalin a cikin Jos babban birnin jihar ta Filato.