PDP ta tsaida Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Image caption Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta tsaida shugaba Goodluck Jonathan a matsayin wanda zai tsaya mata takarar shugabankasa a babban zaben dake tafe

Shugaban kasar Najeriya Dr Goodluck Jonathan ya samu nasara a zaben fidda gwani da jam'iyyar PDP ta gudanar a daren jiya

Dr. Goodluck Jonathan ya samu nasara ne da kuri'u dubu biyu da dari bakwai da talatin da shida yayin da sauran abokan takararsa biyu, wato tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri'u dari takwas da biyar kana kuma Mrs Sera Jibril ta samu kuri'a daya.

Sakamakon zaben na nuni da cewar shugaba Goodluck Jonathan shine zai tsayawa jam'iyyar ta PDP takarar shugabancinkasa a babban zaben dake tafe.

An bi hanyar kebewa kowacce jiha ne akwatin zabe yayin kada kuri'ar, matakin da bangaren tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yace, bai amince da shi ba, bisa zargin cewa an yi hakan ne da nufin tilastawa wasu wakilai zabar wani dan takara saboda ganin-ido.

An dai yi ta cece kuce kan tsarin nan na karba-karba kafin a gudanar da zaben fidda gwanin