Shugabankasar Tunisia yace ba zai sake tsayawa zabe ba

Shugabankasar Tunisia Zine El Abidine Ben Ali
Image caption Shugabankasar Tunisia Zine El Abidine Ben Ali na Tunisia yace ba zai tsaya takara ba a zaben shekara ta 2014

A jawabin da yayi ga al'ummar kasar Tunisia ta gidan talabijin, shugaba Zine el-Abidine Ben Ali yace ba zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar ba a shekara ta 2014.

Shugaban na Tunisia wanda ya shafe fiye da shekaru ashirin da uku yana mulki ba tare da wata adawa mai karfi ba, yayi wannan jawabi ne yayin da tarzomar nuna rashin amincewa da karuwar rashin aikin yi da kuncin rayuwa ta kai ga tsakiyar babban birnin kasar Tunis

Shugaban ya kuma dau alkawarin gudanar da wasu sauye sauye a tsarin siyasar kasar

To sai dai kuma wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasar sunce ba zasu amince da kalaman shugaban ba

An dai dau lokaci mai tsaho ana gudanar da zanga zangar bakin cikin rashin aikin yi a kasar