Matsaloli game da ambaliyar ruwa a Brazil

Ambaliyar ruwa a Brazil
Image caption Ambaliyar ruwa a Brazil

Ruwan saman da ake cigaba da yi kamar da bakin kwarya ya janyo cikas wajen gudanar da aikin ceto a yankin kudu maso gabashin Brazil, inda mutane fiye da 500 suka hallaka, sakamakon ambaliyar ruwa da kuma kwararowar tabo.

A Teresopolis, daya daga cikin garuruwan da lamarin ya fi muni, an dakatar da tashin jirage masu saukar angulu, wanda hakan ya janyo cikas wajen kaiwa ga yankunan da ke kan tsaunuka, wadanda kogin tabon da ke malala ya kewaye.

Gwamnan jahar Rio de Janeiro ya ce, hasashen yanayin da aka yi na kwanaki biyu masu zuwa ba shi da kyau.

Ya bukaci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar kwararowar tabo da su bar gidajensu.