Jonathan ya lashe zaben fitar da gwani na PDP

Jonathan ya lashe zaben fitar da gwani na PDP
Image caption Shugaba Jonathan yana bayani ga mahalatta taron

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta zabi shugaba Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar da zai tsaya mata takara a zaben da za a gudanar nan gaba a kasar.

Shugaban ya samu nasara ne da gagarumin rinjaye a zaben da wakilan jam'iyyar da suka fito daga sassa daban-daban na kasar suka gudanar a daren ranar Juma'a.

Tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar shi ne ya zo na biyu a zaben yayinda Mrs Serah Jibril ta zo ta uku.

Tun kafin a gudanar da zaben dai, bangaren tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar ya yi korafi dangane da tsarin gudanar da zaben inda aka ware wa kowacce jiha akwatinta, batun da suka ce tamkar matsin lamba ne ga gwamnonin jihohi su tabbata shugaba Jonathan ya lashe zaben.

Yadda ta kaya

Shugaba Jonathan ya lashe zaben ne da kuri'u 2,736 abinda ya kusan ninka adadin kuri'un da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu sau uku wato kuri'u 805 yayinda Madam Sarah Jibril ta samu kuri'a daya tak, wadda ke nufin kenan kusan ita kadai ta zabi kanta kenan.

Wannan nasarar da shugaba Jonathan ya samu a jam'iyyar ta PDP ya nuna kenan jam'iyyar ta yi watsi da tsarinta na karba-karbar mulki tsakanin kudanci da arewacin kasar.

Ya kuma ce zaben nasa ya nuna cewa jam'iyyar PDP ta yi magana da murya daya cewa, hadin kan kasa shi ne kan gaba fiye duk wani abu.

A jawabin da ya gabatar bayan an bashi takarar, shugaba Goodluck Jonathan ya yi kira ga abokan takararsa da su hada hannu da shi wajen ganin jam'iyyar ta samu nasara a babban zabe na kasa da za a gunanar a watan Aprilu mai zuwa.

Hada karfi da karfe

"Ku zo mu hada hannu a mtsayinmu na jam'iyya guda, mu nemi kuri'un 'yan Najeriya, mu samar musu da shugabanci na gari a shekaru hudu masu zuwa".

Ya kara da cewa ya kamata 'yan Najeriya gaba daya su hada hannu don kawo sauyi mai ma'ana a kasa.

An yi ta cece-kuce a kan takarar ta shugaba Goodluck Jonathan ganin cewa ya fito ne daga Kudancin kasar.

Inda abokan adawar sa suka jajirce cewa a yanzu lokaci ne da ya kamata dan Arewa ya tsaya takarar shugabancin kasar karkashin tutar jam'iyyar PDP.

Martani

Kawo yanzu dai babu wani martani daga bangaren Atiku Abubakar, game da sakamakon zaben.

Sai dai mai magana da yawunsa Malam Garba Shehu, ya ce "babu wani tabbaci cewa wakilan sun yi zaben cikin radin kansu".

Yace tsarin da aka yi amfani da shi ya ba da damar abi diddigin dan takarar da mutum ya zaba, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

A yanzu dai shugaba Jonathan zai fuskanci 'yan takarar manyan jam'iyyun adawa na kasar wato Janar Muhammadu Buhari wanda jam'iyyar CPC ta riga ta tsayar da shi takarar shugabancin kasar.

Da kuma 'yan takarar da jam'iyyu ACN da ANPP za su tsayar a zabukansu na fidda gwani da za su gudanar.