Shirin rijistar masu zabe ya fara da cikas

Hukumar INEC
Image caption Kwanaki goma sha biyar za a shafe ana gudanar da wannan rijista

Rahotanni daga sassan Najeriya da dama na nuna cewa aikin rajistar masu zabe da Hukumar zaben kasar ta fara a ranar Asabar ya fara da tuntube da musamman na na'u'rori.

A wasu sassan babban birnin tarayya na Abuja , ba a samu damar fara yin rajistar ba har bayan Sallar Azahar.

Wakilin BBC Muhammad Kabir Muhammad wanda ya ziyarci wasu wuraren yin rajistar a Karamar Hukumar Bwari da ke yankin birnin tarayyar, ya ce abubuwa ba su tafi kamar yadda aka tsara ba.

Haka ma wakilin BBC a Sokoto Haruna Shehu Tangaza wanda ya sa ido kan shirin a Yankin Arewa maso Yammacin kasar, ya ce duk kanwar ja ce.

A wasu jihohin ma akwai wuraren da ba a fara rijistar a ranar Asabar din ba kamar yadda aka tsara, saboda matsaloli daban-daban.

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ne, ya bude shirin Rajistar a mahaifarsa ta Ogbia, dake jihar Bayelsa, a inda kuma Shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa, Attahiru Jega ya jagoranci yi masa rajistar.

Sai dai mai magana da yawun Hukumar Nick Dazan ya shaida wa BBC cewa suna kokarin shawo kan tangardar da aka samu.

Ya kara da cewa Hukumar ta yi iya kokarinta illa dai kawai 'yan matsalolin da ba a rasa ba.