An rantsar da shugaban wucin gadi a Tunisia

Sojoji
Image caption Sojoji dauke da bindiga na sunturi a birnin Tunis da kewaye

A kasar Tunisia an rantsar da kakakin Majalisar Dokokin Tunisia a matsayin shugaban wucin gadi bayan da masu zanga-zanga suka tilasta wa shugaba Ben Ali tsere wa daga kasar.

Kuma tuni shugaban rikon ya nemi Fira ministan kasar da ya kafa sabuwar gwamnati kamar yadda gidan talabinjin din kasar ya bayyana.

Sai dai rahotanni sun ce har yanzu ana ci gaba da samun tashin hankali a Tunisia kwana guda bayan tserewar shugaban.

Tun da farko Fira minista Muhammad Ghannouchi wanda ya ke rike da ragamar shugabanci, bayan tafiyar shugaban kasa ya shaida wa gidan talabijin na kasa cewa yana son dawo da bin doka da oda.

Ya ce, zan iya cewa muna cikin wani yanayi mai tsauri. Har yanzu akwai matsalar kwasar ganima da sace-sace, don haka abu na farko shi ne mu kawo karshen hakan.

Akwai rahotannin tashin gobara a gidajen yari a garin Monastir na gabar ruwa, inda mutane sama da arba'i suka mutu.

Majalisar tsarin mulkin Tunisiar ta ce za a gudanar da zabe cikin watanni biyu.

An nemi a zauna lafiya

Rahotanni sun bayyana cewa Shugaban Ben Ali yana kasar Saudi Arabiya.

Kungiyar kasashen Larabawa ta yi kira ga dukkan kungiyoyin siyasar Tunisia da su hada kan su domin samun zaman lafiya a kasar.

Ta yi kira da a kwantar da hankali, ta kuma bukaci kasar ta kasance ta cimma matsaya kan yadda za a kauce ma tashin hankali.

Ahmad Unayes, wani jami'in diplomasiya ne dake zaune a birnin Tunis.

Ya ce: "Muna jin cewa matakin da aka dauka ya yi hanzari, an mika mulki daga wata gwamnati zuwa wata cikin gaggawa".

Duk da yake sabuwar gwamnatin alkawari ce kawai, amma abubuwan da aka tsara suna da kyau, muna fatan za su tabbata.

Tun da farko wani kakakin gwamnatin kasar Qatar ya ce suna mutunta zabin al'ummar ta Tunisia.

Karin bayani