Yakin neman zaben shugaban Nijar

Tutar Nijar
Image caption Tutar Nijar

A jamhuriyar Niger an kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasar da na 'yan majalisar dokoki.

A ranar 31 ga wannan watan na Janairu ne ake sa ran gudanar da zabubukan, bayan zaben kananan hukumomin da aka yi a ranar Talatar da ta wuce.

Kimanin mutane miliyan 6 da dubu 700 ne zasu kada kuri'ar zaben shugaban kasar, daga cikin 'yan takara kimanin goma.

Za su kuma zabi mambobin majalisar dokokin kasar 113.

Sai dai matakin da kotun tsarin mulkin kasar ta dauka, na watsi da takardun wasu jam'iyyu a neman kujerun majalisar dokoki, ya rage wa yakin neman zaben armashi.