Cikas a rajistar masu zabe a Najeriya

Tutar Najeriya
Image caption Tutar Najeriya

A Najeriya yau aka shiga rana ta biyu da fara aikin sabunta kundin sunayen masu kada kuri'a a duk fadin kasar.

Sai dai kuma ana fama da matsaloli daban-daban game da gudanar aikin rajistar.

Ko da yake hukumar zabe ta kasar wadda ke gudanar da wannan aiki, ta ce ana kokarin shawo kan matsalolin.

Matsalolin sun hada da rashin isassun kayayakin aiki, da rashin ingancin na'urorin yin rajistar.