An kai Malam Tanja Mamadou kurkuku

Malam Mamadou Tanja
Image caption Malam Mamadou Tanja

Lauyan tsohon shugaban Nijar Mamadou Tanja ya ce, hukumomi sun kai tsohon shugaban a gidan kurkukun Kollo mai tsananin tsaro.

A da Malam Mamadou Tanjan yana tsare ne a wani gida da ke fadar shugaban kasa a Yamai.

Lauyan ya ce gwamnati bata bada wani dalili ba game da daukar wannan matakin.

A watan Nuwamban da ya wuce, kotun kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, ECOWAS ko CEDEAO, ta umurci a sake shi, saboda a cewar ta, tsarin da ake masa ya sabawa doka.

To sai dai a watan Disamban bara an cire kariyar da doka ta bashi, wanda hakan ya bude hanyar tuhumarsa da yin sama da fadi da wasu kudade.

Kusan shekara daya kenan da sojoji su ka yiwa Malam Mamadou Tanja juyin mulki, saboda kiki kakan siyasar da aka samu a kasar ta Nijar.