Ana cigaba da samun tashin hankali a Tunisia

Kasar Tunisia
Image caption Ana cigaba da samun tashe tashen hankula a kasar Tunisia duk kuwa da tserewar tsohon shugabankasar Zaine Al Abidin Ben Ali

Ana cigaba da fuskantar tashe-tashen hankula akan titunan kasar Tunisia, yayin da kuma shugabannin siyasar kasar ke cigaba da laluben inda kasar zata sa gaba, bayan wanda ya jima yana mulkin kasar, wato Zaine Al Abidin Ben Ali ya tsere.

Fiye da mutane arba'in ne dai suka mutu sakamakon tarzoma da kuma gobara da ta barke a wani gidan yari na birnin Monastir a kasar ta Tunisia

Shugaban majalisar dokokin kasar, Fouad Mebezza, wanda tun farko aka rantsar a matsayin shugaban riko na kasar, ya bukaci Fira Ministan ksar, ya kafa gwamnatin hadin kan kasa.

Kuma wani shugaban 'yan adawa yace, tuni an soma tattaunawar tsakanin bangarorin kasar.

Lamarin na Tunisia dai ya soma yin tasiri a wasu kasashen larabawa, inda a kasar Jordan wasu suka yi zanga-zanga a ofishin jakadancin Tunisian

Shugaban kasar Libya, Kanar Gaddafi shine ya zama shugaban wata kasar larabawa na farko da ya tofa albarkacin bakinsa dangane da tashe-tashen hankulan da ake fuskanta yanzu haka a Tunisian.

A jawabin da yayi ta talabijin, Kanar Gaddafi ya shawarci al'ummar Tunisia su kwaikwayi abinda ya kira, samfurin dimukradiyya irin na Libya, inda iko ke hannun jama'a