Ana gwabza fada a birnin Tunis

Tankunan yaki a birnin Tunis
Image caption Tankunan yaki a birnin Tunis

Dakarun tsaro a Tunisia na gwabza fada tare da wasu da ake zargin masu gadin fadar shugaban kasar ne, a fadar shugaban kasar mai nisan kilomita da dama a arewacin Tunis, babban birnin kasar.

Mazauna yankin sun ce ana yin mummunar musayar wuta da bindigogi.

Praministan Tunisiyar, Mohammed Ghannouchi, ya bayyana a gidan talabijin din kasar inda ya ce, ba za a yi sassauci ga duk wani mutum da ke kokarin yin zango kasa ga tsaron kasar ba.

A ranar Juma'a ne shugaban Tunisiyar Zine al-Abidine Ben Ali ya tsere daga kasar, sakamakon zanga zangar da jama'a suka yi ta yi.

Praminista Ghannouchi da 'yan siyasa na bangaren adawa sun ce, gobe Litinin za su bada sanarwar kafa sabuwar gwamnati.