An kashe malamin zabe a Jos bisa bambancin addini

Tutar Najeriya
Image caption Bambanci ya kara kamari

Wani hari da wasu kiristoci suka kai a yankin tsakiyar Nigeria ga wasu musulmai yayi sanadiyar mutuwar mutane ukku yayin da wasu akalla biyu suka samu raunika.

Rikicin ya barke ne a birnin Jos a lokacin da wasu matasa kiristoci suka kaiwa wasu jami'an zabe musulmi hari, wadanda suke aikin kai kayan rajista gabanin zaben da za a yi a watan APrilu mai zuwa.

An dai hallaka daya daga cikin Malaman zaben, yayin da aka kashe kiristoci matasa biyu a lokacin da yan sanda suka bude wuta domin fasa gungun wadanda suka kai harin.

A cikin watan da ya gabara kawaim, an kashe mutane fiy da dari a yankin na jos a rikice-rikicen addini.