Ana saran kafa sabuwar gwamnati a Tunisia

Firma Ministan Tunisia na ganawa da Ahmed Brahim na jam'iyyar adawa
Image caption Fira Ministan kasar Tunisia Mohammed Ghannouchi na tattuanawa da 'yan adawa domin kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa a yau litinin

Har yanzu dai ana ganin sojoji suna yin sintiri a kan titunan kasar Tunisia dama kusa da gine ginen gwamnati

Ga alamu sojojin dake yin biyayya ga tsohon shugabankasar daya tsere ne suke san kawo cikas a yunkurin da ake yi na kafa sabuwar gwamnati a yau litinin.

Anyi musayar wuta sosai bayan da jamin 'yan sanda sukai kokarin dakatar da wasu mutane dauke da makamai a kusa da hedkiwatar babbar jam'iyyar adawar kasar.

Shugabankasar mai rikon kwarya ya kira wata ganawa ta jam'iyyun siyasar kasar da kuma masu bada shawara, domin tattauna yadda za'a bi a kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa da kuma shirya sabbin zabuka.

Cikin jam'iyyun da shugaban ya tattauna dasu kuwa harda jam'iyyar Progressive Democratic Party wato PDP

Wani babban jami'inta Dr Firas Jabloun y shaidawa BBC cewar sabuwar gwamnatin hadin kan kasar zata baiwa harkar tsaro mahimmanci