Su Atiku ba zuwa kotu kan zaben PDP

Wasu rahotanni daga Najeriya na cewa, tsohon shugaban mulkin sojan kasar, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Janar Aliyu Gusau, sun yanke shawarar cewa ba zasu je kotu ba, akan zaben dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasar na watan Afrilu.

Shugaba Goodluck Jonathan ne ya lashe zaben da aka yi a ranar Alhamis da ta wuce, inda ya kada Alhaji Atiku Abubakar, da kuma Madam Sarah Jibril.

Janar Babangida, da kuma Janar Aliyu Gusau duk sun janye daga takarar ne, domin karfafa takarar Alhaji Atiku Abubakar.