Dan kunar bakin wake ya kashe mutane 50 a Iraqi

Taswirar kasar Iraqi
Image caption Kasar Iraqi ta dade tana fama da tashe-tashen hankula

A kalla mutane 50 ne suka mutu bayan da dan kunar bakin wake ya kai hari a wajen wata cibiyar daukar masu shiga aikin 'yan sanda a garin Tikrit na kasar Iraqi.

A kalla wasu mutanen 50 ne suka jikkata a garin, wanda ke da nisan kilomita 130 a Arewacin Bagadaza.

Wannan shi ne adadi mafi yawa da aka kashe a rana guda tun bayan garkuwar da aka yi wa wata majami'a a watan Oktoba wacce ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 50.

Fadace-fadace sun ragu a Iraqi a 'yan shekarun nan, amma hare-hare sun karu.

Maharin - wanda ke sanye da shimin da aka cika da nakiyoyi - yana tsakiyar wadanda ke neman a dauke su aikin 'yan sanda ne sama da dari.

Jami'ai sun ce mafi yawan wadanda abin ya ritsa da su masu neman shiga aikin 'yan sanda ne.

Birnin Tikrit nan ne mahaifar tsohon shugaba Saddam Hussaini, kuma masu tada kayar baya na da karfi a garin sosai.

'Yan sandan Iraqi da cibiyoyin daukar sojoji - wuri ne da ake yawan kaiwa harin kunar bakin wake, a cewar wakilin BBC Ayoubi Roula a birnin Bagadaza.