Shugaban PDP ya yi murabus

Image caption Tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Dr Ezekwesili Nwodo

Shugaban jam`iyyar PDP mai mulkin Najeriya Dr Ezekwesili Nwodo ya yi murabus daga mukaminsa sakamakon matsin lambar da yake fuskanta.

Tuni dai Kuma Majalisar zartarwar jam`iyyar wadda ta kammala zaman ta na gaggawa a Abuja ta amince da murabus din shugaban.

Farfesa Rufa`i Ahmed Alkali shi ne Kakakin jam`iyyar na kasaya shaida wa wakilin BBC Ibrahim Isa cewa, halayyar da shugaban ya nuna a wurin taron fitar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ne ya sa shi yin murabus.

A yanzu kwamitin zartarwa na jam'iyyar ya umarci mataimakin shugaban na kasa Dr Bello Halliru da ya ci gaba da rike mukamin na wucin gadi.

Haka kuma an nemi tsohon shugaban ya gurfana a gaban kwamitin da'a na jam'iyyar domin bada ba'asi kafin a duba hukuncin da ya kamata a dauka a kansa.

Badakalar Shugabanci

Badakalar ta kunno kai dangane da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, inda wasu kusoshin jam'iyyar a shiyyar Kudu maso Gabashin kasar, suka nemi a yi biris da bukatar tsige shugaban jam'iyyar na kasa daga mukaminsa.

Har wa yau dai shugabannin jam'iyyar ta PDP a shiyyar Kudu maso Gabashin Najeriya, sun bayyana rashin gamsuwarsu da shugaban jam'iyyar na kasa sakamakon zargin da suke yi masa, na yin watsi da kundin tsarin mulkin jam'iyyar, da rashin yin biyayya ga umarnin kotu, ta hanyar bayyana a wajen babban taron jam'iyyar na kasa, wanda aka gudanar a makon da ya gabata a Abuja.

Masu lura da al'amura dai, na ganin wannan sabuwar badakala, ba ta rasa nasaba da tsamar da ake zargin ta shiga tsakanin bangaren shugaban jam'iyyar PDPin na kasa, da kuma wasu kusoshin jam'iyyar a Kudu maso Gabashin Najeriya, a cewar wakilin BBC a Enugu AbduSsalam Ahmed Ibrahim.

Jam'iyyar bata ji dadi ba

Jam`iyyar dai ta ce ta yi na`am da murabus din shugaban ne saboda wani abin da ya yi da ya bata mata rai, inda ya halarci babban taronta na kasa cikin gayyar-sodi, lamarin da ta ce ya so ya bata mata tafiya, alhali yana sane kotu ta dakatar da shi daga mukamin.

Sai dai yayin da jam`iyyar ke dogaro da kutsen da ta ce shugaba mai murabus din ya yi mata a wajen babban taronta a matsayin hujja, wasu rahotanni sun nuna cewa masu iko a kasar ne ke kitsa makircin sauke shugaban da nufin mai da shugabancin jam`iyyar ga `ya`yanta da ke Arewacin kasar.

Ana dai ganin za'a yi amfani da wasu daga Kudancin kasar wajen kiran lallai sai Dr Nwodon ya sauka daga mukaminsa.

Ganin cewa yanzu shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan, wanda ya fito daga Kudancin kasar ya samu tikitin takara a karkashin inuwar jam`iyyar a babban zaben da ke tafe.