Kasashen Larabawa na taro a kan talauci

Amr Mousa, magatakardan kungiyar kasashen Larabawa
Image caption Amr Mousa, magatakardan kungiyar kasashen Larabawa

Babban magatakardan kungiyar kasashen Larabawa, Amr Moussa, yayi wata kakkausar suka akan yanayin tattalin arzikin da ake ciki a kasashen Larabawa, inda ya danganta matsalolin da ake fuskanta a yankin da boren da ya wakana a Tunisia.

A lokacin da ya ke bude wani taron koli a Sharm Al-Shaikh, Amr Moussa, ya yi gargadi akan irin gagarumar matsalar zamantakewar da ke fuskanatar kasashen Larabawa, yana mai cewar talauci da rashin aikin yi da kuma raunin tattalin arzikin da ake fuskanta - sun karya zukatan Larabawa.

Ya ce , juyin juya halin da aka fuskanta a Tunisia, bai fi karfin ya afku a ko' ina ba, sannan kuma bai sha bamban da abin da za su tattauna a taron kolin na su ba.