Kungiyar MEND ta musanta barazanar hari

A yankin Naija Delta na Nijeriya, ana samu bayanai masu sabawa da juna daga kungiyar fafutuka ta MEND, wadda a baya ta fitar da wata sanarwa dake nuna cewa zata kai sababbin hare-hare.

Sai dai a wata sanarwar ta daban kuma, kungiyar ta ce ba ta da hannu wajen barazanar kai hari kan dukiyoyin da masana'antun mai, a yankin na Naija Delta.

A jiya ne dai, Kungiyar, a wani sakon email, ta bada sanarwar cewa, tana shirin kai munanan hare-hare, kan wasu dukiyoyi da kuma kayan jigilar mai a yankin.

Sai kuma a yau wata wasika ta email da Jomo Gbomo ya turo ke nisanta kungiyar da barazanar kai harin.