Harin kunar bakin wake ya kashe mutane 12 a Iraqi

harin bom a Iraqi
Image caption Wasu daga cikin wadanda harin ranar Talata ya ritsa da su

Wasu 'yan kunar bakin wake sun yi amfani motar asibiti wurin kai hari a wata harabar 'yan sanda dake tsakiyar Iraqi, inda suka kashe mutane 12.

Wasu da dama ne suka jikkata a harin na garin Baquba - wanda shi ne na biyu da aka kaiwa 'yan sanda a kasar cikin kwanaki biyu.

A ranar Talata, wani dan kunar bakin wake ya kashe kusan mutane 60 a wani wurin daukar mutane aikin 'yan sanda a Tikrit, mahaifar tsohon shugaba Saddam Hussain.

Fadace-fadace a Iraqi sun ja baya a 'yan kwanakin nan, amma ana ci gaba da fuskantar hare-hare.

Duka birnin na Baquba mai nisan kilomita 65 a Arewa maso Gabashin Bagadaza - da Tikrit matattara ce ta mabiya darikar Sunni da ke adawa da gwamnatin kasar da kuma sojojin kasashen waje.

A wani harin na daban, wani dan kunar bakin wake ya kai hari kan mabiya darikar Shi'a da ke tafiya daga birnin Bagadaza zuwa Karbala, inda ya kashe mutane biyu tare da jikkata wasu 15.