Takaitaccen tarihin Malam Ibrahim Shekarau

Image caption Mallam Ibrahim Shekarau

An haifi Shekarau ne a unguwar Kurmawa da ke jihar Kano, Ya kuma yi karatun Firamare a makarantar Gidan Makama daga shekarar (1961-1967).

Ya yi karantun sakandare a Kano Commercial College daga shekarar (1967-1973) sannan kuma ya garzaya jam'iyyar Ahmadu Bello da ke Zaria daga shekarar (1973-1977) inda ya samu takardar shaidar digiri ta farko.

Bayan da ya kammala karatunsa na jami'a, mallam Ibrahim Shekarau ya yi aikin gwamnati, sannan ya koma dakin karatu inda ya zama malamin lissafi a Government Technical College da ke Wudil a shekarar 1978, bayan shekaru biyu ne kuma ya zama shugaban makarantar Government Day Junior Secondary School a Wudil.

A shekarar 1980 an koma da shi makarantar Government Secondary School da ke Hadejia, sannan Government College Birnin Kudu a 1986, sai kuma Government Secondary School a Gwammaja da kuma makarantar Rumfa College a 1988, duk a matsayin shugaban makaranta.

Daga nana dai mallam Shekarau ya zama mataimakin darakta a harkar illimi a shekarar 1992, bayan kuma shekara guda aka mayar da shi darekta.

Daga nan dai likkafa ta ci gaba inda ya zama babban sakatare a ma'ikatar harkar illimi.

A watan Fabrerun shekarar 2000, malam Shekarau ya koma aikin gwamnati, kafin a koma da shi kwalejin share fagen shiga jam'ia a matsayin babban malamin lissafi.

A nan dai Shekarau ya ajiye aiki da gwamnati bayan ya yi aikin na tsawon watanni 17 a kwalejin.

Siyasa

Ba'a dauki Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wani dan takara da zai yi tasiri ba a zaben gwamnan da aka yi a shekarar 2003 a jihar, amma daga baya kuma sai ya yi tasiri inda ya lashe zaben.

Kuma Malam shekarau ya kafa tarihi inda ya zama gwamna na farko da aka zabe shi a karo na biyu a matsayin gwamna a jihar Kano.

Mai martaba sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya nada shi a matsayin Sardaunan Kano a karon farko a tarihin masauratar Kano.

Malam Ibrahim Shekaru ne dai dan takarar shugaban kasa, karkashin inuwar jam'iyar ANPP a Zaben watan Afrilu na shekarar 2011.