Shugaba Obama ya gana da Shugaba Hu na China

Shugaba Obama da Shugaba Hu
Image caption Shugaba Obama da Shugaba Hu

Shugaba Obama na Amurka ya karbi bakuncin takwaran aikinsa na Kasar China Hu Jintao a birnin Washington inda aka yi wani kasaitaccen buki a harabar fadar White House.

Shugaba Obama ya ce dukkanin kasashen biyu, za su fi samun wadata idan suka hada karfi da karfe, yayin da Mr Hu kuma ya ce dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kai wani sabon mizani a cikin yan watannin nan.

To amma dukkanin shugaban kuma sun yi tsokaci a kan banbance banbancen da ke tsakaninsu.

Mr Obama ya ce tarihi ya nuna cewar an fi samun adalci a duniya, idan aka kiyaye da hakkin kowa da kowa, yayin da shi kuma Mr Hu ya ce, kamata yayi dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ta kasance ta mutunta juna duk kuwa da banbance banbancen tafarkin da kowa ya runguma na ci gaba.

Shugaban na kasar China, Hu Jintao ya kuma gana da Shugabannin harkokin kasuwanci na Amurka, inda ya dauki alkawarin karawa jamaa masu sayen kayyaki karfin saye tare da karfafa musu guiwa ta bukatar kayayyaki.

Shugaban na China ya ce cinikayya tsakanin kasashen biyu ta na da kyakkyawar makoma a nan gaba.

Amurka da Chinar dai suna takaddama akan darajar kudin kasar ta China Yuan, inda China ke watsi da zargin da ake yi mata cewar da gangan ta rage darajar kudinta domin ta taimaka wajen ganin ta na sayar da kayyaki masu yawa zuwa ga kasashen waje.

A waje daya kuma wani babban Jamiin gwamnatin Amurkar ya ce kasashen biyu sun kulla yarjjeniyar cinikayya ta dola biliyan arba'in da biyar.