Tattalin arzikin China ya bunkasa

Tattalin arzikin China ya haura hasashen da aka rika yi masa inda ya karu da kashi goma cikin dari a bara.

Sai dai Kasar ta gaza cimma burinta na rage hauhauwar farashi da kashi uku cikin dari.

China ta ce tattalin arzikinta, wanda shi ne na biyu a girma a duniya, ya habaka fiye da yadda aka zata a bara.

Haka kuma an samu karin ciniki fiye da kaso goma sha takwas.

Bankunan gwamnatin China dai sun saki makudan kudade musamman a bangaren cinikin filaye da gine-gine.