Harin bom ya kashe mutane da dama a Iraqi

Wasu mata 'yan Shi'a
Image caption Wasu mata mabiya darikar Shi'a na ziyara a garin karbala

Wasu bama-bamai a motoci biyu sun fashe a wurare daban-daban a birnin Karbala, inda suka kashe mutane akalla arba'in da biyar, tare da raunata wasu fiye da dari.

Rahotonni sun ce fashe-fashen sun auku ne a gefen birnin, a kan muhimman hanyoyi guda biyu da masu ziyarar addini ke bi zuwa wajen wani bukukuwan addinin.

Kafin sannan, wani harin bom din da aka kai a hedikwatar 'yansanda a birnin Baquba ya kashe akalla mutane ukku.

Kwanaki uku ke nan ana kai hare-hare a sassa daban-daban na kasar ta Iraqi.

Karin bayani