An samu karin matsaloli a aikin rejistar masu zabe a Nijeriya

Shugaban Hukumar zaben Nijeriya, Profesa Attahiru Jega
Image caption Shugaban Hukumar zaben Nijeriya, Profesa Attahiru Jega

A Nigeria har yanzu ana cin karo da matsaloli wajen aikin sabunta rijistar masu zabe.

Wata sabuwar matsala da aka lura da ita yanzu haka ita ce ta yiwa wasu mutanen rejista ba tare da an dauki hoton zanen yatsun su ba.

Haka kuma akwai rahotanni da ke nuna cewa wasu na yin rijistar fiye da sau daya, duk kuwa da cewa hukumomin zaben kasar na gargadin kaucewa hakan.

A bangarenta dai hukumar zaben mai zaman kanta INEC ta ce duk wanda ya yi rijistar ba tare da an dauki hoton zanen yan tsayunsa ba, to ya dauka tamkar bai yi ba ne.

Haka kuma wanda yayi rijistar sama da sau daya, to zai yi biyu babu.