Rajistar masu Zabe a Najeriya

Image caption rajistar masu zabe

Yayinda jama'a a Nigeria ke kokawa da matsalolin da suke fuskanta wajen sabunta rajistar masu zabe, wata sabuwa kuma ita ce halartar yara da shekarunsu ba su kai kada kuri'a ba da zummar su ma a yi mu su rajistar.

Rahotanni daga sassan kasar da dama na nuni da cewa ana samun yaran da shekarunsu basu kai ba, su na halatar wuraren yin rajista.

A mafi yawan lokutan dai yaran suna boye shekarunsu inda suke kari kan shekarunsu na haihuwa.

Dokar zaben kasar dai ta ce masu shekaru goma sha takwas zuwa sama ne kawai suka cancanci samun rijistar.

A baya ma an sha gamuwa da irin wadannan matsalolin na rijistar wadanda shekarunsu ba su kai ba, abinda za'a iya bayyanawa a matsayin wani salo na magudin zabe.

Sai dai hukumar zaben mai zaman kanta, INEC, ta ce ta na aiki da jami'an tsaro don shawo kan matsalar.