Hukumar bincike ta Tarayya ta FBI a Amurka ta kai samame kan yan mafiyar New York

Eric Holder, Sakataren Shara'a na Amurka
Image caption Eric Holder, Sakataren Shara'a na Amurka

Hukumomin gwamnatin tarayya na Amurka sun kama mutane fiye da dari da goma, a abin da Babban Ministan Shari'ar kasar, Eric Holder, ya bayyana da samame mafi girma da aka taba yi a kan kungiyar nan ta masu aikata miyagun laifuka ta Mafiya.

Mr Holder ya ce, "kame-kamen na yau wani muhimmin mataki ne mai karfafa gwiwa, wajen katse hanzarin ayyukan La Cosa Nostra, wato kungiyar ta Mafiya."

Jami'an tsaro fiye da dari bakwai suka shiga aikin kame mutanen a biranen New York, da New jersey da kuma Rhode Island, a jerin samamen da aka kai da jijjifin safiya.