Switzerland ta hana Gbagbo kadarorinsa

Image caption Laurent Gbagbo

Gwamnatin Switzerland ta ce ta hana taba kadarorin da shugaba Laurent Gbagbo na Ivory Coast ya mallaka a kasar.

Mr Gbagbo ya ki yarda ya mika mulki ga Alassane Ouattara, wanda aka yi amannar shi ne ya lashe zaben na watan Nuwamba.

Wannan mataki na zuwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tura karin sojojin kiyaye zaman lafiya 2,000 zuwa kasar domin karfafa ikon 9,800-da suke can.

Fira Ministan kasar Kenya, Raila Odinga ya shaida wa BBC cewa yunkurinsa na sasanta rikicin siyasar kasar ya gaza.

Daga bisani kuma, Fira Ministan Gbagbo, Alcide Djedje ya ce ba zai kara amincewa da Mr Odinga a matsayin mai shiga tsakani ba.

"Muna ganin yana da bangare a rikicin don haka ba zai kara zamo wa manzon Tarayyar Afrika ba," kamar yadda ya ce bayan Mr Odinga ya bar kasar.

Dakarun Majalisar ne dai ke kare Mr Ouattara a otel din da ya ke zaune a birnin Abidjan.

Sakataren Majalisar Ban Ki-moon, ya ce dakarun na fuskantar kalubale daga magoya bayan Ouattara.

"Abin takaici ne Mr Gbagbo ya ki amince wa ya janye shingen da ya sa a otel din da Mr Ouattara ke zaune - kuma wannan ya sa tattaunawar ta rushe."