Amurka da China sun kulla yarjejeniyar kasuwanci

Obama da Hu
Image caption Shuagaba Obama ya tarbi shugaba Hu cikin girmama wa

Gwamnatin Amurka ta kulla yarjejeniyar kasuwanci ta dala biliyan 45 tsakaninta da China, kamar yadda wani jami'i ya bayyana.

Yarjejeniyar ta hada da sayen jiragen sama samfurin Boeing guda 200 a kan dala biliyan 19 da China za ta yi.

Ta zo ne a daidai lokacin da shugaban China Hu Jintao ya ke ziyarar aiki a Amurkan.

Shugaban kamfanin Boeing Jim McNerney, na daga cikin 'yan kasuwar da su ka halarci tattaunawar da shugaba Obama ya yi da shugaba Hu a fadar White House ranar Laraba.

Ayyukan yi

Sauran shugabannin kamfanonin da su ka halarta sun hada da Steve Ballmer na Microsoft da Lloyd Blankfein da Goldman Sachs da Jeff Immelt da General Electric.

Jami'an sun ce yarjejeniyar ta kuma hada da sayen kayayyakin gona na Amurka da na sadarwar salula da kuma na'urar kwamfiyuta, kuma za su samar da ayyukan yi dubu 235,000.

Sauran kamfanonin da za su amfana daga cinikin sun hada da Honeywell da Caterpillar da Westinghouse Electric wanda wani bangare ne na kamfanin Toshiba na Japan.

Sayayyar ta China za ta taimaka wa kamfanin na Boeing, ganin kalubalen da ya ke fuskanta na dakatar da samfurin jirginsa na Dreamliner.

Image caption Shugabannin biyu suna tattauna wa a dakin taro na Ovall

Zai kuma taimaka masa wajen shawo kan tazarar da ke tsakaninsa da kamfanin Airbus, wanda a bara ya ba shi tazarar ciniki ta kashi 52% cikin dari.

Banbance-banbance

Tun da farko Shugaba Obama ya ce dukkanin kasashen biyu, za su fi samun wadata idan suka hada karfi da karfe, yayin da Mr Hu kuma ya ce dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kai wani sabon mizani a cikin 'yan watannin nan.

To amma dukkanin shugaban sun yi tsokaci a kan banbance-banbancen da ke tsakaninsu.

Mr Obama ya ce tarihi ya nuna cewar an fi samun adalci a duniya, idan aka kiyaye hakkin kowa da kowa.

Yayin da shi kuma Mr Hu ya ce, kamata yayi dangantakar da ke tsakani, ta kasance ta mutunta juna duk kuwa da banbance-banbancen tafarkin da kowa ya runguma na ci gaba.

Rikicin darajar kudade

Masana tattalin arziki a Najeriya sun ce ziyarar da shugaban kasar China ya ke yi a Amurka za ta yi tasiri a fannin tattalin arzikin kasashe masu tasowa, kasancewa kasashen biyu su ne mafiya karfin tattalin arziki a duniya.

Sai dai masanan sun kara da cewa cece-kucen da ake yi kan darajar kudade tsakanin kasashen biyu, ba zai yi wata barazana ga bunkasar tattalin arzikin kasashe masu tasowa ba.

Amurka ta dade tana zargin China da karya darajar kudinta domin samun damar kan abokan kasuwancinta.

Sai dai ita ma China ta zargi Amurka da yin hakan, abin da Amurkan ta musanta.

Karin bayani