Italiya ta shiga yamutsi inji fadar vatican

Image caption Firayministan Italiya Silvio Berlusconi

Fadar Vatican ta bukaci 'yan siyasar Italiya su zamo masu kyawawan dabi'u.

Wannan kiran ya biyo baya zargin da ake yiwa firaminista Silvio Berlusconi ne da shirya badala da matasan karuwai.

Wani babban jami'in Vatican, Cardinal Tarcisio Bertone ya ce Italiya ta shiga yamutsi game da batun.

Akan haka coci na jawo hankalin kowa, musamman masu rike da madafun iko a bangaren mulki, ko siyasa, ko shari'a da su rike halaye na kwarai, tare da bin doka.

Alkalan birnin Milan dai sun gaiyaci Mr Berlusconi ya gurfana gabansu game da zargin.

Sai dai, kawo yanzu bai baiyana ko zai amsa kiran ba ko a'a.