'Na yi biris da kashedin da aka yi min kan Iraqi'- Blair

Tsohon Praministan Birtaniya, Tony Blair, ya ce yayi biris da kashedin da Atoni Janar na lokacin yayi masa, cewa, kaiwa kasar Iraki hari ba tare da izinin majalisar dinkin duniya ba, ya sabawa doka.

Mista Blair ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyana a karo na biyu, a gaban kwamitin da ke gudanar da bincike kan irin rawar da Birtaniya ta taka a yakin Iraki.

Tsohon Pira ministan ya ce, ya yi amannar hannunka mai sandan da Atoni Janar din yayi masa, na wucin gadi ne.

Yanke shawarar kaddamar da yaki a Iraqi ba tare da izini karara ba daga kwamitin sulhu na Majalissar Dinkin Duniya, ya zama wani lokaci da ya sauya al'amurra siyasar Birtania ta wannan zamani.

Rarrabuwar kawuwnan 'yan Birtaniya

Babu wani al'amarin da ya rarraba kawunan mutanen Birtaniya kamar shi, bayan rikicin mashigin Suez a farkon shekarun alif dari tara da hamsin.

Haka nan kuma al'amari ne da ya rage kima da kuma karsashin siyasar Pirayi ministan Burtaniya Tony Blair, abun da kuma ya taimaka matuka wajen maye gurbin sa daga karshe da Gordon Brown.

Tsohon Pira Minista Gordon Brown ne ya kafa wannan kwamitin bincike na Chilcot, ko da ya ke da alamun ba dan ya so ba.

Kuma daga irin shaidun da aka fara samu a zagayen farko na zaman wannan kwamiti, ko da yake akwai dari-darin kafa shi tun farko, akwai kawararan shaidun da ke nuna kwamitin na kokarin bin diddigin manya-manyan alamun tambayar da suka kunno kai gabanin kaddamar da yakin.

Rashin bin ka'idojin aiki

Wadannan tambayoyi kuwa sun hada da, dalilin da ya sa, babban Jami'i mai baiwa gwamnati shawara akan harkokin shari'a ya sauya ra'ayinsa akan halascin yakin ba tare da samun wani kuduri na biyu ba na Majalissar Dinkin Duniya.

Image caption Tsohon shugaban Amurka, George Bush da kuma Tony Blair su kai hari Iraq ba tare da izinin Majalisar Dinkin Duniya ba.

Akwai kuma batun ko Mr Blair ya gabatarwa da Amurkawa shawarar farko da gwamnatin Burtaniya ta samu daga lauyoyinta akan cewar yakin bai halasta ba ko kuma a'a. Sannnan mafi muhummanci kuma yau shi ne, kuma bisa wadannan sharudda, Mr Blair ya yiwa Mr Bush na Amurka alkawarin cewar zai marawa Amurka baya a wannan yaki ko da sama da kasa zata hade.

Daya daga cikin babbar matsalar da ake fuskanta shine yadda kwamitin ya kasa samun sukunin ganin wasu muhimman takardu wadanda suka shafi tarurrukan sirrin da aka yi tsakanin Pirayi Minista Tony Blair da kuma Shugaba Bush.

To sai dai duk da yadda yiwa Mr Blair tambayoyi a bainar Jamaa ke da ban sha'awa, babban zakaran gwajin dafi ga wannan kwamitin bincike shi ne rahoton da zai fitar na wucin gadi.

Kwamitin dai yana kunshe da mutane wadanda suka nakalci rubuta rahotanni na bincike, akan irin harkallah da aka yi ta fama da ita gabanin rikicin.

Kuma a yanzu haka tun gabanin a je ko ina, akwai bangarori da dama na gwamnatin Burtaniya, wadanda suka hada da wasu sassa na ma'aikatar leken asirin kasar da suka yi imanin kaddamar da yakin babban kuskure ne.