Gabrielle Giffords ta bar asibiti

Gabrielle Giffords
Image caption Gabrielle Giffords

'Yar majalisar dokokin Amirka, Gabrielle Giffords, wadda kusan makonni biyu da suka wuce aka harbe ta a kai, a lokacin da take ganawa da masu zabe, ta bar asibitin da take kwance a Tucson a jahar Arizona.

Za a kai ta wata cibiya a birnin Houston na Texas, inda za ta ci gaba da murmurewa.

Mutane sun yi layi a kan tituna, yayin da motar asibiti ta dauko ta zuwa wani sansanin sojan Amirka, inda daga can aka dauke ta a jirgin sama zuwa Houston.

Mutane shidda suka hallaka a lokacin harbe harben da aka jikkata Gabrielle Giffords.

Likitoci sun yi gargadin cewa, ko da yake Ms Giffords din na samun sauki sosai, to amma watakila za a kwashe watanni ana yi mata magani.

Kuma lokaci bai yi ba da za a san illar da harbin zai yi ga lafiyar ta a nan gaba.