Ana iya sasanta rikicin Cote d'Ivoire

Raila Odinga
Image caption Raila Odinga

Praministan Kenya, Raila Odinga, ya shaida wa wani taron manema labarai cewa, ko da yake akwai sauran sarari na warware kiki-kakar da aka samu a Cote d'Ivoire ta fuskar siyasa, za a iya daukar matakin soji idan abu ya ki.

Ya ce Laurent Gbagbo, shugaban da ya ki sauka daga mulki, bai ma son yin tattaunawa da abokin hamayyarsa, Alassane Ouattara, ko kuma kawar da kawanyar da ya sanya aka yi wa Hotel din da Alassane Ouattara yake.

A makon gobe ne ake san Mr Odinga zai gabatar da rahoto ga kungiyar Tarayyar Afrika.