An saki dukkan fursunonin siyasa a Tunisiya

Gwamnatin wucin gadi ta Tunisia ta saki dukkan fursunonin siyasa da aka tsare a lokacin mulkin shugaban kasar da aka hambarar, Zine El Abidin Ben Ali.

Wani minista ya sheda ma wani gidan rediyon Faransa cewa tuni ma aka saki tsararrun.

Eric Goldstein na kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, wanda ya je Tunisiar, ya bayyana yadda bukatar jama'ar a kan tattalin arziki ta rikide zuwa neman biyan bukatun siyasa.

Ya ce, "galibi a kan tattalin arziki ne, amma sai 'yan sanda suka yi amfani da harsashe mai kisa, suka kashe matasa maza gwammai, abinda ya harzuka jama'a, ya maida boren zuwa neman biyan bukatu na siyasa."

A jiya ne dai gwamnatin rikon kwaryar ta ce ta dauki matakan amincewa da haramtattun kungiyoyin siyasa a Tunisiyar, da kuma yin ahuwa ga dukan fursunonin siyasa.

A yau ne aka fara zaman makoki na kwana ukku a Tunisiyar, domin mutanen da suka rasa ransu, a lokacin zanga zangar da ta kifar da gwamnatin Ben Ali.