Fira Ministan Ireland ya sauka daga mukamin shugabancin jam'iyyarsa

 Fira Ministan kasar Ireland Brian Cowen
Image caption Fira Ministan kasar Ireland Brian Cowen ya sauka daga kan mukaminsa na shugaban jamiyya

Kasa da mako guda bayan daya lashe kuri'ar nuna goyan baya daga jam'iyyarsa , Prime Ministan kasar Ireland Brian Cowen ya sauka daga kan mukaminsa na shugaban jam'iyyar Fianna Fail Party.

Ya shaidawa taron manema labarai cewar yadda ake cigaba da sukar shugabancinsa, na yin illa ga kokarin da jam'iyyar tasa take yi na shirya babban zaben dake tafe a cikin watan Maris.

Sai dai Yace zai cigaba da rike mukaminsa na Prime Minista har sai lokacin da majalisa ta zabi wanda zai gaje shi.