Tattaunawa kan makaman nukiliyar Iran

Shugaban Iran Ahmedinijad yana duba wata tashar nukiliyar kasar

An shiga rana ta biyu ta tattaunawa da masu shiga tsakani na manyan kasashe shida ke yi a birnin Istanbul na kasar Turkiyya, dangane da shirin nukiliyar kasar Iran.

Bangarorin biyu da ke yin wannan tattaunawar dai sun bayar da bayanan da ke karo da juna dangane da yadda tattaunawar ta kasance, yayin da a ranar Juma'a wakilan Iran suka ce, ana samun cigaba.

Sai dai wani jami'in difilomasiyya na yammacin duniya da ke halartar taron ya ce, basu gamsu da irin dabi'ar da Iran ke nunawa a wajen tattaunawar ba.

Ana dai zargin Iran ne da kera makaman nukiliya a boye, amma Iran din ta sha musanta wannan zargi.