Al Muqtada Al sadr ya koma kasar Iran

Shugaba Mahmoud Ahmadinajad
Image caption Fitaccen malamin addinin nan na Kasar Iraq Muqtada Al sadr ya sake komawa kasar Iran

Rahotanni na cewar fitaccen malamin addin nan na kasar Iraki Muqtada Al Sadr ya koma kasar Iran, kasa da makonni uku bayan ya dawo kasar Iraqi daga gudun hijirar da yayi zuwa kasar ta Iran.

Wata majiya ta shaidawa BBC cewar malamin addinin zai cigaba da karatunsa ne na addinin a kasar ta Iran.

A wani jawabi da yayi a garin Najaf na kasar Iraqin. Muqtada Al Sadr yayi kira ga magoya bayansa da cewar kada su amince da abinda ya kira mamayar Amurka amma sai dai ya gargade su akan daukar makami