An bindige mutane biyu a Maiduguri

Jami'an tsaro a Maiduguri
Image caption Jami'an tsaro a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri sun ce, sojoji sun harbe wani dan achaba har lahira a unguwar rukunin gidaje na gwamnatin tarayya, lokacin da suke binciken ababan hawa a daren jiya.

A taron manema labaran da rundunar sojan a Maiduguri ta kira, Birgediya Janar Ibrahim Ndah Liman ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce jami'an tsaron sun bukaci dan achabar ya tsaya amma ya ki.

Yau da safe kuma wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba, sun bindige daya daga cikin sojojin aka girke a unguwar Jajeri domin samar da tsaro..

Kashe-kashe dai lamari ne ya ki ci ya ki cinyewa a Maidugurin.

Wasu kashe-kashen ana danganta su da kungiyar Boko Haram da kuma 'yan siyasa.