Buhari bai ji dadin batan na'urorin rijistar zabe ba

Janar Muhammadu Buhari
Image caption Janar Buhari bai gamsu da yadda ake aikin rijista ba

Dan takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam'iyyar CPC, Janar Muhammadu Buhari, ya nuna rashin jin dadinsa dangane da yadda aka sace na'urorin aikin rijistar masu kada kuri'a a kasar.

Janar Buharin, wanda ya yanki katinsa na rijista a mazabarsa da ke Daura a jihar Katsina, ya nuna takaicinsa ga yadda tun farko wasu na'urorin aikin rijistar su ka bace a lokacin da aka shigo da su a kasar.

Ya ce dole gwamnati ta dauki alhakin duk korafe-korafen da mutane ke yi kan batan na'urorin aikin rijistar.

Janar Buhari ya yi kira ga shugaban hukumar zaben kasar ya tattabar an gano na'urorin, kuma ya dauki matakai na tabbatar da ingancin zaben da za a yi a watan Afrilu mai zuwa.