Kungiyar Falasdinawa ta kashe Krista a Masar

Cocin Coptic a Masar
Image caption Cocin Coptic a Masar

Kasar Masar ta ce tana da shaidun da suke nuna cewa, masu fafutuka na Falasdinawa a Gaza, wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyar Al-qa'ida, sune suka kai hari a wata mujami'a a birnin Alexandria.

Fiye da mutane ashirin ne suka hallaka a lokacin harin a jajibirin sabuwar shekarar nan.

Ministan harkokin cikin gida na kasar ta Masar, Habib Al-Adly, ya ce ana zargin wata kungiya mai suna 'Army of Islam', ko Rundunar Islama, da kai wannan hari.

Wannan dai yana daga cikin hare-hare mafiya muni da aka kaiwa al'ummar Krista a Masar, a kusan shekaru goma.

Shugaban na Masar, Hosni Mubarak, ya ce a yanzu doka ba za ta yiwa maharan sassauci ba.