Abokin Gbagbo ya sauka daga mukaminsa

Mr Laurent Gbagbo
Image caption Abokin Gbagbo ya sauka daga shugancin bankin Afirka

An tilastawa daya daga cikin makusantan shugaban Ivory Coast, Laurent Gbagbo yin murabus daga kan mukaminsa na gwamnan babban bankin kasashen yammacin Afirka.

Babban bankin ya ce, ya sallami Philippe Henri Dacoury-Tabley daga kan mukaminsa ne saboda ya ki aiwatar da umarnin da aka ba shi na ya daina amincewa da sa hannun Laurent Gabgbo wajen sakin kudade mallakar kasar ta Ivory Coast a bankin.

Tuni dai Laurent Gbagbo ya fitar da dala miliyan dari da sittin daga asusun kasar, kuma zai yi amfani ne da kudin wajen biyan albashin sojoji da kuma cigaba da kasancewa akan mulki.

Laurent Gbagbo ne dai ya nada Phillipne Dacoury-Tabley a mukamin shugaban babban bankin shekaru uku da suka gabata, kuma wasu na ganin Mista Dacoury-Tabley ya ki mikawa Alassane Ouattara ragamar asusun Ivory Coast da ke bankin ne saboda biyayyar da ya ke yiwa Gbagbo.